14 Oktoba 2025 - 08:51
Source: ABNA24
Fursunonin Falasdinawa 154 Da Aka 'Yanto Sun Isa Masar

Ofishin kula da fursunonin Falasdinu ya sanar da cewa fursunoni 154 da aka sako sun isa Masar a lokacin musayar fursunoni da gwamnatin Isra'ila.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya bayar da rahoton cewa: Bisa yarjejeniyar, za a fitar da wadannan mutane daga Falasdinu bayan an sako su gidajen yarin Isra'ila zuwa wasu kasashen.

Motocin bas din fursunonin Falasdinawan da aka sako sun isa Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan bayan tsauraran matakan tsaro da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauka na hana bukukuwa.

Bayan kammala sakin fursunonin Isra'ila 20 masu rai bisa matakin farko na yarjejeniyar Gaza, motocin bas na farko dauke da fursunonin Palasdinawa da aka sako sun isa zirin Gaza da Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan.

Your Comment

You are replying to: .
captcha